Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak ya rasu
2020-02-25 19:39:42        cri
Rahotanni daga kafofin watsa labaran kasar Masar sun ce tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ya rasu a yau Talata bayan ya sha fama da jinya, yana da shekaru 91 a duniya.

Kafin rasuwar sa, Mubarak ya mulki Masar na tsawon shekaru kusan 30, kafin daga bisani ya yi murabus, sakamakon boren da ya karade kasar a shekara ta 2011. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China