Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID -19 a Masar ya karu zuwa 59
2020-03-10 10:32:11        cri

Masar ta sanar da karin mutane 4 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar, zuwa 59.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar Khaled Mujahid ya ce mutanen 4 da suka hada da 'yan asalin kasar 3 da wata bakuwa 1, sun yi mu'amala da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a baya.

Ya bayyana cewa, bayan samun kulawar da ta dace a asibitin da aka kebe su, gwajin da aka yi wa mutane 20 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu, ya nuna a jiya Litinin cewa, yanzu ba sa dauke da cutar.

Ya ce yanayinsu ya daidaita, kuma har yanzu suna asibitin da aka kebe domin masu cutar, inda suke samun kulawa bisa ka'idojin hukumar lafiya ta duniya WHO.

A ranar Lahadi ne Masar ta sanar da mutuwar mutum na farko sanadiyyar cutar numfashi ta COVID-19, wanda ya kasance wani dan Jamus mai shekara 60 da ya je kasar kwanaki 8 da suka gabata domin yawon bude ido. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China