Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar da Sudan da Habasha za su yi taron ministoci kan batun madatsar ruwan Nile a Washington
2020-02-25 10:55:28        cri
Gwamnatin kasar Masar ta sanar a jiya Litinin cewa, za'a gudanar da taron ministocin harkokin waje da na albarkatun ruwa na kasashen Masar, Sudan da Habasha game da batun madatsar ruwa ta GERD na kogin Nile da ake takaddama kansa a ranakun 27-28 ga watan Fabrairu a birnin Washington na Amurka.

Cikin sanarwar, majalisar mulkin kasar Masar ta ce, kwamitin koli na Nile, wanda firaminista Mostafa Madbouly ke jagoranta, ya gudanar da taro a ranar Litinin domin yin nazari game da ci gaba na baya bayan nan da aka samu kan batun GERD game da shirye shiryen taron tattaunawar da za'a gudanar a Washington wanda ake sa ran shugaban bankin duniya zai halarta.

Tattaunawar, tana zuwa ne bayan shafe shekaru masu yawa an gaza cimma matsaya kan batun, lamarin ya sa tilas aka tsara wani shirin yarjejeniya kan batun madatsar ruwan, wanda ake fatan za'a karkare, kana a rattaba hannu kan yarjejeniyar daga karshe a nan gaba cikin wannan watan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China