Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar da Sudan sun zanta game da madatsar ruwa ta Habasha
2020-03-16 12:11:34        cri
Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya zanta da mataimakin shugaban majalissar koli ta Sudan Mohamed Hamdan Dagalo, game da batun ginin babbar madatsar ruwan GERD ta kasar Habasha, wadda ake ginawa a kogin Nilu da ya ratsa kasashen uku.

Fadar mulkin Masar ta sanar da gudanar da wannan tattaunawa a jiya Lahadi. Yayin tattaunawar, an zanta game da ci gaban ginin wannan madatsar ruwa ta GERD bisa matsayar yarjejeniyar da aka cimma ta kasashe 3 ta birnin Washington, wadda kuma Masar ta sanyawa hannu, kamar dai yadda kakakin shugaban kasar Masar Bassam Rady ya tabbatar.

Cikin sanarwar da aka fitar, Rady ya ce Mr. Dagalo ya jinjinawa Masar, bisa kokarin ta a fannin tabbatar da tsaro da samar da daidaito a Sudan.

Bayan ganawa da shugaba Al Sisi, Mr. Dagalo ya ce kasar Sudan na da ruwa da tsaki a madatsar ruwan GERD, za ta kuma kasancewa mai shiga tsakani wajen tattaro ra'ayoyi da tabbatar da cimma matsaya.

Ya ce bayan kammalar ta, madatsar ruwa ta GERD za ta samar da wutar lantarki da za ta kai megawatt 6,000, za kuma ta kasance madatsar ruwa dake samar da lantarki mafi girma a Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China