Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya za su dawo da daukar matakai kan 'yan bindiga a jihar Zamfara
2020-03-26 10:20:21        cri

Gwamnan jihar Zamfara dake yankin arewa maso yammacin Najeriya, Bello Matawalle, ya bayyana cewa, dakarun kasar za su dawo da matakan da suke dauka na kai hare-hare kan 'yan bindiga a jihar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, gwamnan ya ce, matakin bude wuta da tuni aka dauka kan 'yan bindiga jihar, ya fara haifar da babban sakamako, inda aka yi nasarar ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su, har ma an kammala duba lafiyarsu a asibitin gwamnatin jihar, an kuma mika su ga iyalansu.

Gwamnan ya nanata haramcin da gwamnatinsa ta sanya kan kungiyar 'yan banga, da aka fi sani da "San sa kai". Za kuma ta sanya kafar wando guda da duk wani basaraken gargajiya da aka samu yana goyon bayan ayyukan kungiyar da aka haramta, ciki har da tube masa rawani.

Ya ce, dawo da matakan na soja, ya kai ga damke masu taimakawa 'yan bindigar da bayanai guda 7, kuma nan ba da dadewa ba, za a kai su Abuja don fuskantar laifin da suka aikata.

A cikin watanni biyun da suka gabata, ayyukan fashi da makami da satar mutane, sun sake dawo wa a jihar. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China