![]() |
|
2020-03-23 19:32:59 cri |
A cewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar NCDC, mutumin mai shekaru 67 da haihuwa ya dawo kasar ne daga Birtaniya inda ya je domin neman magani.
Cibiyar ta ce baya ga cutar ta COVID-19 mutumin na fama da wasu cututtukan da suka hada da sankarar da suka shafi kananan halittun jini da ciwon suga, shi ya sa yake jinyar sankara.
Kawo yanzu, Najeriya ta samu wadanda suka kamu da cutar COVID-19 kimanin 36 a kasar. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China