Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bangarori daban-daban na Amurka sun ki yarda da shirin Donald Trump na sassauta matakin kandagarkin COVID-19
2020-03-25 13:03:24        cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya zanta da manema labarai na gidan telibiji na Fox da yammacin jiya Talata agogon Amurka, inda ya bayyana cewa, yana shirin sassauta matakin kandagarkin cutar COVID-19, kuma yana fatan jihohi daban-daban na kasar za su bude kofarsu kafin tsakiyar watan Afrilu, sai dai nan da nan bangarori daban-daban suka nuna rashin jin dadinsu game da furucin.

Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Patricia D'Alesandro Pelosi ta nuna cewa, kamata ya yi Trump ya saurari shawarar masana kimiyya, sannan ya bayyana ra'ayinsa a gaban jama'a bisa tushen kimiyya da shaidu.

Ban da wannan kuma, mai kamfanin Microsoft wato Bill Gates, ya ce farfado da ayyukan tattalin arziki cikin sauri mataki ne maras kyau. Saboda ganin halin da Amurka ke ciki, yin cikakkiyar kebancewa na tsawon makoni 6 zuwa 10, mataki ne mafi dacewa na hana yaduwar cutar.

Ko da yake gwamnatin tarayyar kasar na da nata ra'ayi, jihohi daban-daban na kasar na ci gaba da daukar matakai mafi tsanani don kebe jama'a cikin gidansu. Ya zuwa yammacin jiya, jihohi 13 sun sanar da dokar kebe kai a cikin gida, wadda ta shafi mutane fiye da miliyan 150. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China