Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kalamai masu alaka da COVID-19 dake nuna kyamar baki da wariya ba su dace ba
2020-03-24 10:42:40        cri

Jami'in MDD na musammam mai nazari kan nau'ikan wariyar launin fata da kyamar baki, Tendayi Achiume, ya ce ya yi takaicin jin jami'an gwamnati na amfani da kalaman dake da alaka da wariya da kyamar baki kan cutar COVID-19, yana mai cewa, alakanta cutar da wani yanki abu ne da bai dace ba.

Ya ce yayin tattaunawa da kafafen yada labarai, dole ne jami'an gwamnatoci su tabbatar da amsarsu kan annobar COVID-19, ba ta da alaka da kyamar baki ko bambancin launin fata, sannan dole ne su kaucewa irin wadannan kalaman cikin duk wani sako ko dabarunsu.

Ya kara da cewa, alakanta sunan kwayar cutar da wani yanki zai kai ga nuna wariyar launin fata da kyamar baki. Inda ya ce zai sa a rika kyamar wadanda ake ganin Sinawa, da kuma jama'ar sauran kasashen gabashin Asiya.

A cewarsa, irin wannan ya janyo kalaman kiyayya da na kin ba da hidima ko kuma cin zarafi.

Ya ce matsaloli irin na annobar kwayar cutar Corona, na tunatar da cewa, dukkan bil adama na da alaka da juna, kuma rayuwarsu ta dogara da juna. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China