Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taro ta bidiyo tsakanin ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashen G20
2020-03-24 10:37:32        cri

An yi taro ta kafar bidiyon hoto tsakanin ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashen G20 a jiya Litinin, inda suka tattauna kan illar da cutar COVID-19 ke yi wa bunkasuwar tattalin arzikin duniya, tare da amincewa su hada kai don magance kalubalolin da cutar ke haifarwa a duniya.

Mahalarta taron sun kai ga matsaya daya, kan sa ido kan yaduwar cutar a duniya da kuma illar da take yi wa kasuwanni da tattalin arziki, tare kuma da amincewa da daukar matakai cikin hadin kai don tinkarar wannan mumunar cuta. Ban da wannan kuma, sun yarda da kiran irin wannan taro na bidiyo lokaci-lokaci, don ci gaba da tattauna matakan da suka wajaba a dauka don tinkarar wannan kalubale a duk fadin duniya.

A sa'i daya kuma, babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira a gun wani taron manema labarai da aka yi a jiya a Geneva cewa, kamata ya yi kasashen G20 su hada kansu da cika alkawarin da suka yi na siyasa, don tinkarar wannan cuta. A cewarsa, ana bukatar kasashe daban-daban su cika alkawarinsu a siyasance, wajen daidaita batun karancin kayayyakin kandagarkin cutar a duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China