Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a samu sabon rahoton kamuwa da cutar COVID-19 ta cikin gida a fadin kasar Sin ba
2020-03-19 10:52:17        cri

Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar da cewa ba a samu sabon rahoton kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 ta cikin gida a duk fadin kasar Sin ba a ranar Laraba.

A cewar hukumar lafiyar kasar, ta samu rahoton sabbin mutane 34 da suka kamu da cutar ta COVID-19 wadanda dukkansu sun shigo kasar Sin ne daga kasashen ketare a ranar Laraba.

Baki daya jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasar Sin ya kai 80,928 ya zuwa ranar Laraba, ya kunshi har da marasa lafiya 7,263 wadanda ake ci gaba da ba su kulawa, kawo yanzu an sallami majinyata 70,420 daga asibiti bayan sun warke daga cutar, kana mutane 3,245 cutar ta hallaka a duk fadin kasar Sin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China