Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alhamis ba a samu sabon wanda ya harbu da cutar COVID-19 a babban yankin Sin ba
2020-03-20 10:37:26        cri
Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta ce a dukkanin babban yankin kasar Sin, ba a samu ko da mutum daya, da ya harbu da cutar COVID-19 a ranar Alhamis ba.

Hukumar wadda ta yi wannan tsokaci a yau Jumma'a, ta ce mutane 39 da aka samu dauke da cutar a ranar, dukkanin su sun shigo da ita ne daga ketare.

A wani ci gaban kuma, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da cewa, rashin sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin, babbar nasara ce da aka cimma.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China