Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabbin mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a babban yankin kasar Sin ya kai mutum 13
2020-03-18 13:52:20        cri

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar da cewa, jiya Talata karin mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 ya kai 13 a babban yankin kasar, daga cikinsu 12 sun shigo ne daga ketare, yayin da karin mutane 11 suka mutu sakamakon cutar. Abin lura shi ne, babu sabon mutumin da ake zaton ya kamu da cutar a lardin Hubei a wannan rana, kuma gaba daya mutanen da ake zaton sun kamu da cutar a lardin sun ragu har zuwa sifiri.

An ce, ya zuwa karshen jiya Talata, yawan mutane da suka warke daga cutar a babban yankin kasar Sin ya kai 69,601, yayin da yawan mamata ya kai 3,237, kuma gaba daya yawan mutanen da aka ba da rahoton kamuwa da cutar ya kai 80,894.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ba da rahoton cewa, ya zuwa karfe 5 na yammacin jiya agogon Beijing, yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya ban da kasar Sin, ya kai 97,996, daga cikinsu 4,195 sun rasu.

Alkaluman da cibiyar shawo kan cututtuka ta kasashen Afrika ta bayar na nuna cewa, ya zuwa karfe 10 da rabi na daren jiya, agogon Beijing, kasashen Afrika 30 sun sanar da bullar cutar, kana yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 457. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China