Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jagoranci taron shawo kan cutar COVID-19 da batun bunkasa tattalin arzikin kasa
2020-03-19 13:03:43        cri

A jiya Laraba shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jagoranci taron nazarin hanyoyin da kasar ke bi wajen ayyukan kandagarki, da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, da kuma batun bunkasa tattalin arzikin kasar a gida da waje.

Shugaba Xi ya ce ana ci gaba da fadada matakan kandagarki da shawo kan wannan annoba, kana ana ta gaggauta farfado da ayyukan masana'antu, da rayuwar al'umma ta yau da kullum.

Xi ya nuna cewa, dole ne a dage wajen tabbatar da nasarar da aka riga aka samu, a yakin da kasar ta sha da wannan cuta. Daga nan sai ya bukaci dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, da su karfafa musaya da hadin gwiwa da kasashe daban daban, wajen tunkarar wannan annoba, tare da samar da tallafi ga sassan dake bukata iya iyawarta.

Har ila yau, ya umarci da a ci gaba da samar da kariya, da lura ga rayuka da lafiyar Sinawa dake zaune a kasashen ketare. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China