Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijer ta tabbatar da rahoton bullar cutar COVID-19 a karon farko
2020-03-20 11:13:17        cri
Ma'aikatar kula da lafiyar al'umma ta jamhuriyar Nijer ta sanar a jiya Alhamsi cewa, an samu rahoton wanda ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a karon farko a kasar.

Sanarwar da ma'aikatar lafiyar kasar ta rabawa manema labarai ta ce, majinyacin 'dan shekaru 36, kuma 'dan asalin Nijer ne wanda a kwanan nan ya yi tafiye tafiye zuwa kasashen Togo, Ghana, Cote d'Ivoire da Burkina Faso.

Sanarwar ta ce, tuni aka garzaya da mutumin asibiti don kula da lafiyarsa kuma a halin yanzu ba ya cikin yanayi mai tsanani.

A wani labarin kuma, ita ma kasar Chadi ta samu rahoton wanda ya kamu da cutar a karon farko.

Kafar yada labaran kasar Alwihda Info ta rawaito fadar shugaban kasar Chadi ta tabbatar da cewa, a ranar Alhamis an samu rahoton wanda ya kamu da cutar COVID-19 a karon farko a kasar.

An samu bullar cutar ne a jikin wani fasinja 'dan kasar Morocco wanda ya shiga kasar daga birnin Douala, na jamhuriyar Kamaru. Tuni jami'an lafiyar kasar sun dukufa wajen baiwa marar lafiyar magani, kamar yadda sanarwar ofsihin shugaban kasar ta ayyana, sai dai ba ta yi cikakken bayani kan lamarin ba.

Gabanin samun rahoton farko na mutumin da ya kamu da cutar, gwamnatin kasar Chadi ta ba da umarnin rufe dukkan filayen jiragen saman kasa da kasa dake kasar a ranar Laraba, da nufin dakile bazuwar cutar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China