Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Nijeriya ya karu zuwa 12
2020-03-20 10:48:46        cri
An tabbatar da samun sabbin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a jihar Lagos, cibiyar harkokin kasuwanci ta Nijeriya a jiya Alhamis, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu a kasar zuwa 12.

Shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Chikwe Ihekweazu ne ya tabbatar da batun ga manema labarai jiya a fadar gwamnatin kasar dake Abuja, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan yaki da cutar.

A cewar kwamishinan lafiya na jihar Lagos, Akin Abayomi, sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da wadanda suka taho da ita daga ketare da kuma wadanda suka samu a cikin kasar.

Kwamishinan ya ce, a yanzu, suna bibiyar mutane sama da 1,300 domin sanin yanayin lafiyarsu, yana mai cewa adadin wadanda ake bibiyar na karuwa.

Kawo yanzu, 10 cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Nijeriya na jihar Lagos, inda aka samu daddaya a jihohin Ogun da Ekiti dake yankin kudu maso yammacin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China