Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara gwada allurar riga kafin cutar COVID 19 kan Bil Adama
2020-03-18 12:54:42        cri

Da misalin karfe 8 na daren Litinin, rukunin manazarta karkashin jagorancin malama Chen Wei, ta sashen nazarin kimiyyar aikin jiyya ta soji karkashin kwalejin nazarin kimiyyar aikin sojan kasar Sin, ya fara gwada allurar rigakafin da ya harhada kan Bil Adama.

Tun isowar su birnin Wuhan a ran 26 ga watan Jarairu, rukunin malama Chen Wei ya hada kai da kamfanoni masu karfi dake wurin, don yin nazarin sabuwar allurar rigakafin cutar COVID 19, bisa nasarar da aka samu wajen harhada allurar rigakafin cutar Ebola.

An ce, a daren ran 16 ga wata, rukunin ya samu izinin gwada sabuwar allurar rigakafi kan Bil Adama, kuma za a gudanar da wannan aiki bisa matakai daban daban.

A yayin tattaunawarta da wakilin CMG, Malama Chen Wei ta ce bisa ka'idojin kasa da kasa, da kuma dokokin kasar Sin, Sin ta kammala shiri tsaf, na samar da wannan allura mai yawa, tare da tsaro da inganci matuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China