Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu karin mutane 21 da suka kamu da cutar COVID-19 a babban yankin Sin
2020-03-17 10:33:17        cri

Hukumomin lafiya a kasar Sin, sun ce sun karbi rahoton sabbin mutane 21 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar, kana karin mutane 13 sun rasu sakamakon kamuwa da cutar a jiya Litinin. A daya hannun kuma, ana lura da wasu karin mutanen 45 domin tantance ko suna dauke da cutar ko a'a.

A dai wannan rana, an sallami mutane 930 daga asibiti bayan sun warke daga wannan cuta, yayin da kuma wadanda suke cikin matsanancin halin rashin lafiya sakamakon harbuwa da ita ya ragu da mutum 202, inda a yanzu adadin su bai haura 2,830 ba.

Bugu da kari, hukumar lafiyar kasar ta ce an samu karin mutane 20 da suka shiga kasar Sin dauke da cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China