Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaki da cutar COVID-19 cikin hadin gwiwa ita ce kadai hanyar kawar da ita tsakanin al'ummun kasa da kasa
2020-03-13 19:56:56        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce cutar COVID-19 ba ta da wani shinge, don haka aiki cikin hadin gwiwa tsakanin sassan kasa da kasa ne kadai, hanyar kawo karshen wannan annoba.

Geng na wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa yau Juma'a a nan birnin Beijing. Ya ce ya dace a kawar da ra'ayin nuna ware kai, da nuna kyama, ko kaskantar da wani sashi, a kuma fadada hadin kai tsakanin kasa da kasa.

Bayan taron jami'an tsare tsare karo na 2 na taron birnin Riyadh, na kasashen kungiyar G20, an fitar da takardar bayan taron game da cutar COVID-19, game da hakan, Geng Shuang ya yi nuni da cewa, Sin a shirye take ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya, wajen yaki da wannan cuta karkashin lemar G20, da ma sauran dandali daban daban na kasa da kasa. Ya ce ko shakka babu, za a kai ga cimma nasara. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China