Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Annobar cutar COVID-19 tana shafar daukacin kasashen duniya
2020-03-13 20:04:23        cri
A yau Juma'a, yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana shafar daukacin kasashen duniya, a don haka birnin Beijing, yana samar da tallafin kayayyakin kandagarkin annobar ga sauran biranen ketare.

Rahotanni sun nuna cewa, birnin Beijing ya sanar da cewa, zai samar da tallafin ga birnin Seoul na Koriya ta Kudu, da biranen Tokyo da Yakohama na Japan, da kuma birnin Teheran na Iran.

Geng ya ce, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, birnin Shanghai, da lardunan Shandong, da Zhejiang, da Jiangxi, da Jilin, da Anhui, da Jiangsu, da Henan, da sauran kananan gwamnatocin wuraren dake fadin kasar Sin, sun riga sun samar da tallafin kayayyakin yaki da cutar ga biranen ketare, wadanda suka kulla huldar sada zumunta tsakaninsu, duk da cewa kasar Sin tana kokarin dakile annobar a cikin kasarta, amma tana son jure wahalhalun da take fuskanta, domin samar da tallafi ga kasashe masu bukata. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China