Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sanar da rahoton sabbin mutane 20 sun kamu da cutar COVID-19 a fadin kasar
2020-03-15 16:32:03        cri
Hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar a ranar Lahadi cewa ta samu rahoton sabbin mutane 20 sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a dukkan yankunan kasar, kana sabbin mutane 10 sun mutu a sanadiyyar cutar ya zuwa ranar Asabar.

A cewar hukumar lafiyar, dukkan sabbin mutanen da suka kamu da cutar da kuma wadanda suka mutun daga birnin Wuhan ne, babban birnin lardin Hubei da cutar tafi kamari.

Haka zalika, an samu wasu sabbin mutanen 39 da ake zaton sun kamu da cutar, in ji hukumar lafiyar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China