![]() |
|
2020-03-10 21:07:37 cri |
Bana ake cika shekaru 20 da kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kuma kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Najeriya a fannoni daban daban, tare kuma da taimakawa Najeriya wajen ci gaban masana'antu da tabbatar da dauwamammen ci gaba.
A nasa bangare, Sanata Adamu Mohammed Bulkachuwa, ya bayyana cewa, gwamnati da jama'ar kasar Sin, sun dauki matakai a jere domin dakile annobar, har ma sun rasa babbar moriyarsu, don haka ya kamata daukacin al'ummomin kasashen duniya su jinjinawa kokarinsu, haka kuma su koyi daga fasahohin da suka samu, ta yadda za a hana bazuwar annobar.
Ya ce majalisar dattijan Najeriya, tana son kara karfafa cudanyar dake tsakaninta da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, tare kuma da bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a fannonin gina kayayyakin more rayuwar jama'a, da inganta samar da amfanin gona, da ci gaban yankunan cinikayya maras shinge yadda ya kamata. (Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China