Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu mutum na biyu da ya kamu da cutar COVID-19 a Najeriya
2020-03-09 19:38:38        cri
A yau Litinin ne ministan ma'aikatar lafiya ta Najeriya Osagie Ehanire, ya tabbatar da samun mutum na biyu da ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar. Kaza lika cibiyar shawo kan cututtuka masu yaduwa ta kasar NCDC, ita ma ta tabbatar da wannan labari ta sakon twita da ta wallafa. Cibiyar ta ce mutumin na 2, ya yi cudanya ne da mutum na farko da ya shiga kasar dauke da cutar a jihar Ogun.

NCDC ta ce ana ci gaba da gwada dukkanin wadanda suka yi cudanya da mutum na farko da ya shiga kasar dauke da cutar, a wani mataki na dakile yaduwar ta. Ana kuma ci gaba da killace mutanen 2 da ake da tabbacin sun harbu da cutar.

Mutum na farko dai baturen Italiya ne, wanda ya shiga Najeriya a ranar 25 ga watan Fabarairu daga birnin Milan, ya kuma shiga kasar ne domin ziyarar kasuwanci ta dan lokaci, kafin daga bisani a gano yana fama da cutar ta COVID-19. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China