Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai da rashin adalci da Amurka ke nunawa 'yan jaridar Sin dake kasar
2020-03-13 13:58:38        cri

Kungiyar manema labarai ta kasar Sin ta fitar da wata sanarwa a kwanan baya, inda ta yi Allah wadai da kuma nuna matukar rashin jin dadinta kan matsin lamba da kuma bambancin da Amurka ke nunawa 'yan jaridar kasar Sin dake kasar.

Ta ce, Amurka na kara matsin lamba kan kafofin yada labarai na kasar Sin dake kasar, har ta dauka matakan nuna bambanci kan takardun iznin shiga kasar da 'yan jaridar kasar Sin da suka nema, da takaita ayyukansu a kasar, abin da ya keta 'yanci da muradunsu na neman labarai a ketare yadda ya kamata. Kungiyar ta yi matukar Allah wadai da kuma nuna rashin jin dadi kan hakan tare da yin kira ga Amurka da ta dakatar da matsin lamba a siyasance bisa tunanin yakin cacar baki da nuna bambanci, da kuma dakatar da matakai maras kyau da take dauka na keta 'yanci da muradu kan 'yan jaridar kasar Sin dake Amurka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China