Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kasashe na koyon fasahohin Sin na yaki da cutar COVID-19
2020-03-09 11:40:42        cri

A halin yanzu, kasashen Italiya da Koriya ta Kudu da Iran da sauransu sun dauki matakai na killace yankunan dake fama da annobar COVID-19, dakatar da darussa a makatantu da sauran aikace-aikacen taruwar mutane domin hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Kuma dukkan matakan da suka dauka an tabbatar da tasirinsu a kasar Sin.

A safiyar ranar 8 ga wata, firaministan kasar Italiya Giuseppe Conte ya sa hannu kan wata doka, da ke sanar da killace babban yankin Lombardia da wasu larduna 14 a sauran yankuna guda hudu na kasar Italiya. Kasar Italiya ita ce kasa ta biyu bayan kasar Sin, wadda ta dauki matakan hana zirga-zirgar mutane a wuraren dake fama da cutar mai tsanani.

Haka zalika kuma, kasashen Koriya ta Kudu da Iran da wannan cuta ta bulla a kasashensu, su ma sun koyi wasu fasahohin kasar Sin.

Kwanan baya, shugaban tawagar masanan da hukumar kiwon lafiyar WHO ta turawa kasar Sin, kana, mashawarcin shugaban hukumar WHO Bruce Aylward ya bayyana cewa, matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19 sun kasance abin koyi ga kasa da kasa. Da an yi amfani da fasahohin kasar Sin, da babu bukatar da sauran kasashe su fara aikin yaki da annobar daga tushe. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China