Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministar harkokin gasar Olympics ta Japan: IOC ne ke da ikon jinkirta gasar wasannin Olympics ko a'a
2020-03-12 14:08:28        cri

Jiya Laraba, ministar kula da harkokin gasar wasannin Olympics ta kasar Japan Hashimoto Seiko ta bayyana cewa, kwamitin gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, wato IOC ne yake da ikon yanke shawara ko za a jinkirta gasar wasannin Olympics ta birnin Tokyo ko a'a.

Hashimoto Seiko wadda ta fara shaidawa majalisar dokoki a makon da ya gabata cewa, watakila a jinkirta gasar wasannin Olympics na birnin Tokyo, amma ta ce, soke ko kuma jinkirta gasar abu ne da ba za a iya tunaninsa ba, amma kwamitin IOC zai iya yanke shawara kan wannan batu.

A wannan rana kuma, Hashimoto Seiko ta ce, 'yan wasa su ne abu mafi muhimmanci cikin gasar wasannin Olympics na birnin Tokyo, a halin yanzu, suna shirya gasar Olympics wadda aka gudanar sau daya cikin shekaru hudu, soke gasar, ko kuma jinkirta gasar zai zama abin da ba za su iya yin zato ba.

Ta kuma kara da cewa, a ganin mu, abu mafi muhimmanci a halin yanzu shi ne, gwamnati ta rika ba da labarai na gaskiya, ta yadda kwamitin IOC zai iya tsai da kuduri kan batun yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China