Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da Shinzo Abe
2019-12-24 09:50:15        cri

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Japan Shinzo Abe, a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, a halin yanzu ana fuskantar babbar damar raya dangantaka tsakanin Sin da Japan. Kuma raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin wannan sabon zamani, na da bukatar tabbatar da ra'ayoyin bangarorin biyu kan manyan tsare-tsare, da daukar matakan da za su dace, da kuma habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata kasashen biyu su karfafa mu'amalar dake tsakaninsu a fannin al'adu, da kara fahimtar juna tsakaninsu kan aikin tsaro da kuma sauke nauyinsu a harkokin kasa da kasa. Xi Jinping ya ce yana maraba ga Shinzo Abe, bisa ziyarar sa a kasar Sin, tare da halartar taron ganawar shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu karo na 8. Ya ce, bisa kokarin da shugabannin kasashen biyu suka yi, ana ci gaba da kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Japan. Ya ce "ya kamata mu daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa yanayin duniya, da ka'idojin girmama juna da kuma karfafa mu'amalar dake tsakaninsu, ta yadda za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, yayin da ake cimma moriyar juna". Haka kuma, ya dace bangarorin biyu su kiyaye dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kare 'yancin ciniki na duniya, domin kafa tsarin ciniki na kasa da kasa mai bude kofa ga waje.

A nasa bangare kuwa, Shinzo Abe ya ce, karuwar mu'amalar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu a bana, ta inganta fahimtar juna dake tsakanin kasashen biyu. Shi ya sa, ake fuskantar yanayi mai kyau wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Japan, tana da muhimmiyar ma'ana wajen kiyaye zaman lafiya, da zaman karko da ci gaba na kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China