Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi shawarwari tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Japan
2019-12-07 16:06:14        cri
Jiya Jumma'a, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma daraktan ofishin kwamitin kula da harkokin ketare na kwamitin tsakiya Yang Jiechi, da shugaban hukumar bada tabbacin tsaron kasar Japan Shigeru Kitamura, sun shugabanci taron tattaunawa mai muhimmancin gaske karo na 7 a tsakanin kasashen biyu a birnin Beijing.

A yayin taron tattaunawar, Yang ya bayyana cewa, ya kamata a tsaya kan manufar kasancewar bangarori daban daban, da hada kai don tinkarar hadarurrukan da duniya ke fuskanta, da kuma hada kai don kiyaye tsarin kasa da kasa da MDD ke zama ginshikinsa da tsarin cinikayya na bangarori da dama dake bisa tushen ka'idojin hukumar WTO. Kana da kara kokari tare don ciyar da dunkulewar tattalin arzikin shiyyar gaba, ta yadda za a iya tabbatar da wadata da farfadowar yankin Asiya.

Gaba daya, bangarorin biyu suna ganin cewa, a yanzu haka dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Japan na samun kyautatuwa. Nan gaba kuma zasu kara kokari wajen samar da muhalli mai kyau don bada tabbaci ga manyan ayyukan diplomasiyya da za a gudanar a tsakaninsu a shekara mai zuwa. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China