Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Japan da koriya ta kudu a yakin da ake yi da COVID-19
2020-02-26 20:57:24        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da kasashen Japan da Koriya ta kudu, a yakin da ake faman yi da cutar numfashi ta COVID-19, tana da kuma aniyar samar da tallafi ga kasashen 2 gwargwadon karfinta a wannan fanni.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne a yayin taron menema labarai da ya gudana a yau Laraba, lokacin da aka yi masa tambaya game da yanayin da ake ciki, game da yaduwar cutar a kasashen 2. Ya ce Sin na yin duba na tsanaki game da yaduwar cutar a kasashen 2. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China