Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin: Taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu karo na 8 taro ne na hangen nesa bisa manyan tsare-tsare
2019-12-25 20:13:46        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang ya bayyana cewa, taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu karo na 8 taro ne na hangen nesa bisa manyan tsare-tsare, wanda ya nuna alkibla da ma tsara abin da ake fatan cimmawa a alakar kasashen uku cikin shekaru goma dake tafe.

Ya ce, "Taron ya nuna alkibla da ma tsara abin da ake fatan cimmawa a alakar kasashen uku cikin shekaru goma dake tafe. Na farko zurfafa hadin gwiwa. Kasashen uku sun amince su karfafa alaka a fannonin kare muhalli da matsalar sauyin yanayi,lafiya, tsoffi, kirkire-kirkire, wasanni, matasa da sauransu gami da fadada harkokin da suka shafi muradunsu. Na biyu, nacewa da yin komai a bayyane, kare tsarin kasancewar bangarori daban-daban cikin hadin gwiwa da 'yancin cinikayya, da gaggauta sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki na shiyya (RCEP) da hanzarta yin shawarwari kan yankin cinikayya maras shige tsakanin kasashen uku, da yayata shirin dunkulewar tattalin arziki na shiyya. Na uku, jagorantar harkokin shiyyar tare. Kasashen uku sun kuma amince su hada kansu kan harkokin yankin gabashin Asiya da mayar da hankali kan yankin Asiya da Fasifik, da kara tuntubar juna a harkokin kasa da kasa da na shiyya, da jagorantar harkokin hadin gwiwar shiyya, da bullo da tsarin hadin gwiwar gabashin Asiya wanda zai biya bukataun kasashen shiyyar, da kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun ci gaba gami da kyakkyawar makoma a shiyya da ma duniya baki daya (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China