Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin:Cutar COVID-19 ba ta kawo illa ga jerin ayyukan masana'antun kasar ba
2020-03-11 20:42:21        cri
A yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai cewa, annobar cutar COVID-19, ba ta kawo babbar illa ga tattalin arzikin kasar Sin ba, sai dai wasu ayyuka na kankanin lokaci kawai, kuma kawo yanzu ba a fitar da jerin ayyukan masana'antun kasar zuwa ketare ba.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin tana mallakar cikakken tsarin kere-kere mafi inganci a duniya, tsarin da ke taka babbar rawa a jerin ayyukan masana'antun duniya, a don haka kasashen duniya suna cike da imani kan jerin ayyukan masana'antu, da jerin ayyukan samar da kayayyaki, da kuma makomar tattalin arzikin kasar Sin.

Geng Shuang ya ci gaba da cewa, yanzu haka kasar Sin ta samu sakamako a bayyane wajen dakile annobar, kuma sannu a hankali, kamfanonin kasar sun koma bakin aiki, ciki har da kamfanoni masu jarin waje, kuma ana iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana samun farfadowa a kai a kai, duk wadannan sakamako sun samar da tabbaci ga gudanarwar jerin ayyukan masana'antu a fadin duniya. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China