Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka sun yi tsayuwar daka tare da Sin a yakin da take yi da cutar COVID-19
2020-03-10 20:00:08        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasashen kungiyar bunkasa kudancin Afirka ko SADC, sun gudanar da wani taro na ministocin lafiya a kasar Tanzania. Yayin taron, wakilan kasashen sun jinjinawa kwazon kasar Sin na yaki da take yi da cutar COVID-19, kuma kasashen na SADC, sun sha alwashin ci gaba da mara baya, da hada gwiwa da Sin domin cimma nasara.

Geng Shuang ya ce a yau, kasashen Afirka da al'ummun su, na tare da kasar Sin a wannan yaki, wanda hakan ya nuna irin kawance da 'yanuwantaka dake haifar da taimakon juna tsakanin sassan biyu.

Geng ya kara da cewa, a halin yanzu, kasashen Afirka na fuskantar barazanar yaduwar cutar, tuni kuma cutar ta bulla a wasu kasashen nahiyar. Don haka Sin a shirye take, ta karfafa matakan ta na kandagarkin yaduwar wannan cuta, da karfafa hadin gwiwa da taimako ga nahiyar Afirka. Kaza lika za ta samar da tallafin kwarewa, da ba da agaji da ya dace, a fannin ayyukan kiwon lafiya da kare hadurra, a matakin yankuna da na kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China