Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Abubakar Ayuba Isah: Akwai darussa da ya kamata kasashen duniya su koya daga kasar Sin a fannin yakar cutar COVID-19
2020-03-11 10:30:29        cri


A yayin da kasar Sin da ma duk duniya baki daya ke ci gaba da ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da Abubakar Ayuba Isah, wani dalibi daga jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na farko a fannin kasuwanci a jami'ar nazarin albarkatun man fetur dake kudu maso yammacin kasar Sin a birnin Chengdu, ko kuma Southwest Petroleum University a turance.

A zantawar tasu, malam Abubakar Ayuba Isah ya ce yanzu suna ci gaba da karatu ta kafar sadarwar Intanet, kuma yana gamsuwa sosai da managartan matakai da jami'arsa gami da gwamnatin kasar Sin ke dauka domin ganin bayan annobar. Har wa yau, malam Abubakar Ayuba Isah ya ce akwai bukatar kasashen duniya su koyi kwarewar da kasar Sin ke da ita wajen yakar wannan cuta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China