Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya ta ce babu sabon wanda ya kamu da cutar COVID-19 a kasar
2020-03-07 16:32:39        cri
Gwamnatin Nijeriya ta ce ya zuwa yanzu babu wanda aka gano ya kamu da cutar numfashi ta COVID-19, daga cikin mutane 61 da suka yi mu'amala da wanda ya kamu da cutar, a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.

Ministan lafiya na kasar, sagie Ehanire, ya shaidawa wani taron manema labarai jiya a Abuja cewa, har yanzu ana bibiyar mutane 21 da mai cutar ya yi mu'amala da su a Lagos, da kuma wasu 40 da ya yi mu'amala da su a jihar Ogun dake makwabtaka da Lagos din.

Ya kara da cewa, gwamnatin Nijeriya ta zage damtse wajen kare yaduwar cutar ta hanyar cibiyar shiryawa tunkarar annoba a bangarori daban daban, dake karkashin hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar wato NCDC.

Kawo yanzu, Nijeriya ta kafa dakunan gwaji 5 dake iya gwajin cutar COVID 19 a cikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China