Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Najeriya za ta farfado da bikin kamun kifi Argungun don bunkasa yawon bude ido
2020-03-04 20:54:01        cri
Ministan watsa labarai da al'adu na Najeriya Lai Mohammed, ya bayyana cewa, gwamnati za ta dawo da bikin kamun kifi da al'adu na Argungun da ya yi suna a duniya, da nufin bunkasa harkokin yawon bude ido, bayan shekaru 10 da dakatar da bikin.

Ministan wanda ya bayyana haka ga taron manema labarai a Abuja, ya ce bukukuwan kasa da kasa kamar bikin kamun kifi na Argugum dake tafe, wani bangare ne na kirkire-kirkire cikin sassan da gwamnatin tarayyar kasar ta dogara da su wajen fadada tattalin arzikin kasar don kaucewa dogaro da mai.

Ministan ya ce, wadannan bukukuwa, ba ma kawai suna bunkasa tattalin arziki ba, har ma suna samar da guraben ayyukan yi, musamman ga mata da matasa.

A ranar 15 ga watan Maris ne, za a kaddamar da bikin kamun kifi da al'adu, yana mai cewa, bikin yana daya daga cikin bukukuwan da jama'a ke halarta a Najeriya, kuma biki mafi tsufa, na zuriyoyi da dama.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China