Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aike da sakon jinjina ga mata masu aikin yaki da cutar COVID-19 a ranar mata ta duniya
2020-03-08 15:53:37        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon nuna kwarin gwiwa ga mata masu ayyukan yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 da sauran bangarori, a yayin da ake bikin ranar mata ta kasa da kasa a yau Lahadi.

Jami'an kiwon lafiya mata suna aiki ba dare ba rana, sun dukufa don yakar annobar cutar numfashi domin ceto mutanen da suka kamu da cutar ta COVID-19, sun nuna jajurcewa da sadaukar da kansu, in ji shugaba Xi.

Mata 'yan jam'iyya, 'yan sanda, da masu yaki da yaduwar cututtuka, da ma'aikatan kula da harkokin unguwanni, da 'yan jaridu, da masu aikin sa kai suna sauke nauyin dake bisa wuyansu cikin himma da kwazo, suna aiki babu gajiyawa, suna gudanar da ayyuka masu wahala, kuma suna bayar da babbar gudunmowa wajen dakile annobar cutar bisa ayyukan da suke gudanarwa, in ji Xi.

Shugaba Xi ya bukaci jami'ai mata da su kara kaimi wajen cimma nasarar yaki da cutar COVID-19, su kara jajurcewa, kuma su kare kawunansu ta hanyar kimiyya, kuma su ci gaba yin aiki tukuru don cimma nasarar kawar da annobar cutar da ta barke.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China