Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za'a kammala aikin kafa tsarin shawagin taurarin dan Adam na Beidou bada jimawa ba
2020-03-10 13:44:54        cri
Da misalin karfe 7 da minti 55 na yammacin jiya Litinin, aka yi nasarar harba wani tauraron dan Adam na shawagi na 54 na tsarin Beidou a cibiyar harba taurarin dan Adam na Xichang dake kasar Sin.

Kana, kasar Sin za ta kara harba wani tauraron dan Adam na shawagi a watan Mayun bana, al'amarin da ya sa kasar za ta kammala aikin harba dukkanin taurarin dan Adam na shawagi a cikin tsarin na Beidou.

Tsarin Beidou, wani tsarin shawagin taurarin dan Adam ne mai inganci da kasar Sin ta gina, wanda ya bambanta da na sauran wasu kasashe, kamar su Amurka da Rasha da na Turai. Irin wannan tsari na Beidou na iya samar da hidimomi ga duk fadin duniya, a fannin tsare-tsaren zirga-zirga.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China