Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta harba sabon tauraron BeiDou
2019-06-25 14:12:13        cri

Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam na BeiDou zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Xichang dake lardin Sichuan na kasar da misalin karfe 2:09 na safiyar yau, agogon wurin.

Tauraron wanda aka harba akan linzamin Long March 3B, zai rika kewayawa ne a lokaci guda da duniyar kasa. Kuma shi ne na 46 na dangin BeiDou kuma na 21 na samfurin BeiDou-3.

Bayan kammala gwajin kewaye kewaye, sabon tauraron zai yi aiki da sauran taurarin BeiDou da ke kewaye domin tabbatar da sahihancin aiki da inganta mamaye wurin da suke aiki.

Cibiyar fasahar kera kumbunan sararin samaniya ta kasar Sin ce ta kera sabon tauraron da hadin gwiwar Cibiyar nazarin linzaman taurarin dan Adam, karkashin hukumar kula da kimiyya da fasahar kere-keren sararin samaniya ta kasar Sin.

Harba tauraron shi ne aiki na 307 da jerin Linzaman Long March suka aiwatar. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China