Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar da hidimomin tsarin Beidou zuwa sama da kasashe da yankuna 120
2019-12-27 20:55:50        cri
Kasar Sin ta fitar da hidimomin tsarin shawagin tauraron dan-Adam na BeiDou-3 (BDS-3) na kasar zuwa sama da kasashe da yankunan 120.

Mai magana da yawun shirin na BDS, Ran Chengqi, ya shaidawa taron manema labarai cewa, tsarin na Beidou ya shiga wani sabon zamani na harkar hidimar kasa da kasa, tsarin da ya amfani yankunan ASEAN, kudancin Asiya da gabashin Turai da yammacin Asiya da Afirka, a fannin aikin gona ba tare da wani kuskure ba,da gine-gine na zamani da aikin gina tashoshi na zamani.

Ya ce, kasar Sin ta yi ta yayata ingancin tsarin na BDS da sauran tsare-tsaren zirga-zirga ta yadda zai amfani masu cin gajiyarsa a duniya baki daya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China