Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: An gano yaduwar cutar COVID-19 a sama da kasashe da yankuna hamsin baya ga kasar Sin
2020-03-09 10:21:34        cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana yayin rahoton rana-rana da ta ke bayarwa game da yanayin cutar numfashi ta COVID-19 a jiya cewa, an gano yaduwar cutar a wasu karin kasashe guda 7, jimillar kasashe da yankuna hamshin da uku ke nan bayan kasar Sin.

Sabbin kasashen bakwai da wannan cuta ta bulla, sun hada da Cambodia, da Austria,da Hungary, da Masar, da Peru, da Bulgaria da kuma Maldives. Ya zuwa karfe 10 na safiyar ranar Lahadi agogon tsakiyar Turai, an tabbatar da mutane 105,586 da suka kamu da cutar a fadin duniya, karuwar mutane 3,656 kan na ranar Asabar, ciki har da sabbin mutane 3,610 da suka kamu da cutar a wajen kasar Sin.

Daga cikin mutane 24,727 da aka tabbatar sun kamu da cutar a wajen kasar Sin, 484 sun mutu sanadiyar cutar, karuwar mutane 71 da cutar ta halaka, idan aka kwatanta da na ranar Asabar.

Ya zuwa ranar Lahadi da safe, an ba da rahoton bullar cutar a kasashen Bulgaria, da Costa Rica, da Tsibiran Faroe da Guiana din Faransa, Da Maldives da Malta, da Martinique da Jamhuriyar Moldova karon farko cikin sa'o'i 24, adadin da ya kawo yawan kasashe da yankunan da cutar ta bulla a wajen kasar Sin ya zuwa 101.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China