Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta tabbatar da bullar cutar Corona a karon farko a kasar
2020-02-15 15:44:43        cri
Ma'aikatar lafiya ta kasar Masar, ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Corona a kasar, a jiya Jumma'a.

Kakakin ma'aikatar Khaled Mujahid, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, gwaji ya nuna cewa wani bako na dauke da cutar Corona, inda ya ce batun bai yi tsanani ba, domin cutar ba ta fara nuna alamu ba. Sai dai kuma, bai bayyana asalin kasar bakon ba.

Khaled Mujahid ya ce an sanar da hukumar lafiya ta duniya nan take, yana mai cewa an dauki dukkan matakan da suka kamata bisa hadin gwiwar hukumar ta WHO. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China