Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sallami mutane 1,535 da suka warke daga cutar COVID-19 a babban yankin kasar Sin a Lahadi
2020-03-09 10:17:39        cri
Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, jiya Lahadi, an sallami mutane 1,535 da suka kamu da cutar COVID-19 daga asibiti, bayan sun warke, a babban yankin kasar Sin.

Hukumar ta kara da cewa, ya zuwa jiya Lahadin, jimilar mutane 58,600 aka sallama daga asibiti.

Har ila yau, zuwa jiyan, jimilar mutane 80,735 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a babban yankin kasar Sin, yayin da wasu 3,119 suka mutu sanadiyyar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China