Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birnin Lagos ya dauki matakan dakile yaduwar cutar COVID-19
2020-03-03 10:02:32        cri

Ma'aikatar lafiya ta birnin Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya, ta ce tana daukar matakai 3 na tunkarar kalubalen bazuwar cutar numfashi ta COVID-19, ciki hadda matakan kula da lafiya, da tsaro da kuma bincike.

Da yake tsokaci game da hakan yayin wani taron manema labarai, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya ce yana da kwarin gwiwa game da matakan da jihar ke dauka domin tunkarar annobar.

Tuni dai gwamna Sanwo-Olu ya ziyarci cibiyar killace abubuwa masu iya zama hadari ga lafiyar bil Adama, wadda ke asibitin lura da masu dauke da cututtuka masu yaduwa dake Yaba ko IDH, inda aka killace dan Italiyan nan da ya harbu da cutar ta COVID-19.

Gwamnan ya ce, jihar sa za ta ci gaba da aiwatar da matakan kandagarki, da dakile yaduwar cutar daga mutum zuwa mutum. Ya ce "Ina matukar farin ciki da karfin shirinmu, da matakan tunkarar cutar da muka tanada, don tabbatar da dakile ta a Najeriya".

Daga nan sai gwamnan ya bayyana cewa, jihar Lagos ta riga ta daga darajar asibitin IDH a matsayin shirin ko ta kwana, na ko da yawan wadanda cutar ta harba za su karu. (Saminu Hassan )

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China