Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin ya kai 139
2020-03-05 13:09:12        cri

Bisa labarin da hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayar, a ranar 4 ga wannan wata, yawan sabbin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a kasar Sin ya kai 139, yawan sabbin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar ya kai 31. Ya zuwa ranar 4 ga wannan wata, adadin mutanen da suka kamu da cutar a kasar Sin ya kai 80409, kuma adadin mutanen da aka sallame su daga asibiti bayan da suka warke ya kai 52045, sai kuma adadin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar ya kai 3012.

A daya bangaren kuma, bisa sabon rahoton da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta fitar a ranar 4 ga wannan wata, ya zuwa karfe 10 na safiyar ranar 4 ga wata bisa agogon tsakiyar Turai, yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasashe 76 na duniya ban da kasar Sin ya kai 12,668, kana yawan mutanen da suka mutu ya kai 214. Kasashen Argentina, da Chile, da Poland, da kuma Ukraine, sun gano mutum na farko da ya kamu da cutar a kasashensu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China