Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin kolin JKS ya kira taron nazarin yaki da cutar COVID-19 da tabbatar da rayuwar al'umma
2020-03-04 21:57:56        cri
Zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin ya kira taro a yau Laraba, don nazarin yanayin kandagarki da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 da ayyukan tabbatar da zaman rayuwa da raya tattalin arziki. Babban daraktan kwamitin kolin Xi Jinping ya shugabanci taron.

Xi Jinping ya nuna cewa, yanzu ana samun kyautatuwar yanayin kandagarki da shawo kan cutar, kuma ana gaggauta dawo da aikin samar da kayayyaki da zaman rayuwa, wajibi ne a inganta da habaka halin da ake ciki, don cimma burin hanzarta farfado da tattalin arziki da zaman al'umma yadda ya kamata. Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasar Sin ta ci gaba da yin taka tsan tsan kan annobar, a waje guda kuma a karfafa hadin kai tare da kasashen duniya a fannin yaki da annobar, da daukar nauyin dake wuyanta a matsayinta na wata babbar kasa.

Taron ya kuma nuna cewa, ya kamata a inganta farfado da ayyuka da samar da kayayyaki a yayin da ake kokarin kara bude kofa ga kasashen ketare, da tabbatar da zaman karko a fannonin cinikayyar waje da jarin waje, da kuma habaka kasuwannin duniya da suka shafi fannoni daban daban. Kana ya kamata a ba da tabbaci ga farfado da ayyukan manyan kamfanoni wajen samar da kayayyaki, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki na duniya baki daya. Baya ga haka, a tabbatar da dokar zuba jari na baki 'yan kasashen waje, da taimakawa kamfanoni masu jarin waje wajen warware matsalolin da suke fuskanta a fannin farfado da ayyukansu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China