Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta tabbatar da kyautata tattalin arziki da zamantakewa ta hanyar inganttun dabaru a bangarori 6
2020-03-04 10:25:20        cri

Kasar Sin za ta inganta dabarun kyautata ayyukan muhimman bangarori 6, wadanda suka hada da tsayayyen aikin yi da fannin hada-hadar kudi da cinikayya da kasa da kasa da zuba jari a ketare da jari a cikin gida da kuma ingancin kasuwanni, domin tunkarar annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ta barke da kuma tabbatar da kyautatuwar tattalin arziki da zaman takewa.

An dauki wannan mataki ne yayin taron majalisar gudanarwar kasar Sin da ya gudana jiya Talata, karkashin Firaministan kasar, Li Keqiang.

A cewar Firaministan, tun bayan kaddamar da dabarun kyautata bangarorin 6, sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da hadin gwiwa tsakanin hukumomi, da nufin tabbatar da muhimman alkaluman tattalin arziki na matakin da ya dace. Ya ce akwai yuwuwar fuskantar manyan kalubale a bana, don haka akwai bukatar inganta dabarun domin kyautata ayyukan bangarorin 6.

Taron ya kuma jaddada bukatar kara inganta matakan dakile yaduwar annobar da raya tattalin arziki da zamantakewa. Har ila yau, ya kuma bukaci daukar matakan da za su mayar da hankali ga karfafa bangarorin 6, ta yadda za su shawo kan illar annonbar a kan tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China