Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana baiwa yan kasar Sin cikakken goyon baya a kokarin yaki da cutar coronavirus, in ji mataimakin shugaban hukumar AU
2020-02-09 17:09:58        cri

A yau Lahadi aka fara gudanar da taron kolin kungiyar tarayyar Afirka a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha. Kafin taron, mataimakin shugaban hukumar zartaswar kungiyar, Mr. Thomas Kwesi Quartey ya tattauna tare da wakilin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), inda ya jinjinawa kasar Sin kan kokarin da take yi wajen dakile yaduwar cutar novel coronavirus, kuma a cewarsa, kungiyar zata nuna cikakken goyon baya ga al'ummar Sinawa, don cimma nasarar shawo kan cutar. Ya kuma yabawa gwamnatin kasar Sin bisa namijin kokarin da take yi wajen samar da kayayyaki da fasahohi, da irin nasarorin da ta cimma.

A game da taron kolin kungiyar da za a fara a yau, ya ce taken taron shi ne "Kawar da hare-haren bindiga, don samar da kyakkyawan yanayin ci gaban nahiyar Afirka", taron zai mayar da hankali kan batutuwan zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka. A ganinsa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya, kuma fasahohin da kasar ta samu ya dace kasashen Afirka su yi koyi.

Mr.Thomas Kwesi Quartey ya kuma bayyana godiya ga kasar Sin bisa gudummawar da ta samar ga kasashen Afirka, ya ce kungiyar tarayyar Afirka tana son ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin ta fannoni da dama. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China