Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmancin binciken kimiyya wajen dakile COVID-19
2020-03-03 10:09:21        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin fadada binciken kimiyya, ta yadda hakan zai kai ga shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 da Sin ke fama da ita.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kuma jagoran hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar, ya yi tsokacin ne, yayin da yake rangadi jiya Litinin, a kwalehjin ilimin likitanci ta soji, da kuma tsangayar ilimin likitanci dake jami'ar Tsinghua a nan birnin Beijing.

Shugaba Xi ya kara da cewa, ya zama wajibi a dauki bincike kan cutar COVID-19 da matukar muhimmanci, don haka ya bukaci hanzarta ci gabansa, don shawo kan ayyuka masu wahalarwa, don gane da kandagarki da kuma matakan shawo kan cutar ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce akwai bukatar samo alluran rigakafin cutar masu inganci da nagarta, da magunguna, da kuma kayan bincikenta, ta yadda za a samu zarafin yaki da ita yadda ya kamata.

Kaza lika ya bukaci amfani da ilimin fasaha mai zurfi mallakar kasar, wanda za a ci gaba da amfani da shi bayan kawo karshen cutar. A daya bangaren kuma ya bukaci da a karfafa matakan sanya ido na kasa baki daya, masu nasaba da aukuwar annobar, da samar da dokoki da ka'idoji, da fadada bincike, da samar da kwararru da za su taimakawa kasar wajen tunkarar ayyukan gaggawa na kiwon lafiyar al'umma. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China