Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu aikin sa kai na ba da babbar gudunmawa wajen yaki da cutar COVID-19 a Wuhan
2020-03-06 14:16:42        cri

Tun bullowar cutar COVID-19, mataki mafi kyau na magance kamuwa da cutar shi ne zama a cikin gida ba tare da fitowa ba, amma wasu mutane suna sanya abun rufe baki da hanci, da safar hannu, su shiga aiki a unguwanni da asibitoci, duk da cewa su ba masu aikin jiyya ko 'yan sanda, ko ma'aikatan unguwa ba ne, suna aikin sa kai.

Lokacin da ake namijin kokarin gina asibitin Huoshenshan, masu aikin fasaha 'yan uwa Wei Feng, da Wei Chao, sun tuka injin hakar kasa da suke da shi zuwa wurin aiki. Masu aikin sa kai da dama kamar wadannan 'yan uwa biyu, sun ba da tabbaci ga kammala asibitin cikin lokaci, ta yadda masu fama da cutar suke iya samun jinya a kan lokaci sakamakon kafuwar wannan asibiti.

Mai aikin sa kai Yang Jie na aikin sufurin kayayyakin jinya, ban da wannan kuma, yana aikin fasahar harhada injin tallafin numfashi, da kuma robat mai kashe kwayoyin cuta. A wadannan lokuta

kuwa, injuna da ya yi sufuri, da kuma harhadawa sun kai fiye da dubu.

Mai aikin sa kai Xiao Lin a birnin Wuhan, ban da sufurin masu aikin jiyya tsakanin gidajensu da asibitoci, yana kuma samarwa wadanda suka kamu da cutar magunguna, kuma ya dauki bidiyoyin halin da ake ciki a birnin. A cikin bidiyon da ya dauka, an iya ganin yadda mazaunan Wuhan suke rayuwa, matakin da ya baiwa mutane kwarin gwiwa wajen cimma nasarar yaki da cutar.

Duba da cewa, masu aikin sa kai suna bayyana tunanin sa kai wato ba da himma da sada zumunci, da kuma taimakawa juna, hakan tamkar ababen more rayuwa na musamman ne ga birnin Wuhan. Sun fito ba tare da fargaba a gabanin barkewar cutar ba, da ba da tallafi gwargwadon iyakacin karfinsu, don taimakawa wajen farfado da birnin Wuhan. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China