Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan kimiyya da fasaha na taimakawa wajen kandagarki da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 a nan kasar Sin
2020-03-03 19:42:35        cri

"Makami mafi karfi na dan Adam wajen yaki da cututtuka, shi ne kimiyya da fasaha, dan Adam kuma ba zai yi watsi da matakai na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkiren fasaha ba a yayin da suke tinkarar manyan hadurra da bala'u."Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bayyana haka a yayin da yake duba ayyukan nazarin kimiyya game da kandagarki da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Beijing.

Masana kimiyya da fasahar kasar Sin sun yi amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam da fasahar lissafi ta zamani, don tabbatar da jerin kwayoyin halittar gado na cutar a cikin wata guda, kana sun sanar da wannan nasara da suka cimma ga duniya, hakan ya inganta nazarin sabbin magunguna da allurar rigakafin cutar. A yayin da yake ziyara a lardin Sichuan na kasar Sin, babban mashawarci na babban daraktan kungiyar WHO, Bruce Aylward ya ga yadda tawagar masu nazarin ilmin yaduwar cuta dake yankunan masu wuyar zuwa ta yi amfani da fasahar 5G don mu'amala da kwararru na lardin, wannan ya burge shi sosai, inda ya ce, hadin kan hanyar gargajiya da kimiyya da fasahar zamani na taka muhimmiyar rawa.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China