Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bayyana ma'anar al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam a aikace
2020-03-03 20:48:03        cri

"Ina godiya ga daukacin Sinawa da suke fuskantar rashin walwalar rayuwa kamar yadda suka saba, wannan shi ne sadaukarwar da suka yi, domin hana yaduwar cuta, kuma wannan babbar gudummawa ce da suka bayar ga daukacin bil Adama.

Wannan shi ne tsokacin da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi game da yanayin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ke ciki.

Yanzu cutar numfashi ta shafi kasashe sama da 60, a yayin da kasashen duniya ke tinkarar annobar, sun kara fahimtar namijin kokarin da kasar Sin ke yi wajen kiyaye tsaron lafiyar duniya baki daya.

Bayan bullar cutar numfashi ta COVID-19, a yayin da yake zantawa da shugabannin kasashen waje ta wayar tarho, ko ganawa da baki ko kuma ba da amsa ta wasiku ga abokan kasashen waje, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha ambaton ra'ayin "Al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama", inda ya jaddada cewa, ba kawai kasar Sin ta dauki nauyin tsaro da lafiyar jama'arta ba, har ma da batun lafiyar al'ummar duniya baki daya.

Bayan bullar cutar, nan da nan kasar Sin ta tabbatar da na'uin cutar da jerin kwayoyin halittar gado na cutar tare da bangarori daban daban.

A sa'i daya kuma, kasar Sin ta gayyaci tawagar kwararru ta hukumar WHO don gudanar da bincike a kasar, da nufin fahimtar yanayin yaki da cutar da kasar ke ciki a dukkan fannoni.

Rahoton da kwararrun Sin da na ketare suka bayar, ya ba da muhimmin jagoranci ga kasashen duniya a fannin kandagarki da shawo kan cutar.

A hakika, a yayin da kasar Sin ke kokarin shawo kan cutar a cikin kasar, a waje guda kuma tana namijin kokari don taimakawa kasashe da ba su da fannin aikin jinya mai inganci da wadanda ke cikin hali mai tsanani na yaki da cutar.

Ga misali, kwanan baya cibiyar shawo kan cututtuka ta kasar Sin ta hada kai tare da wasu hukumomi, ciki har da WHO, don taimakawa kasashen Afirka wajen gudanar da ayyukan kandagarki da shawo kan cutar. A cikin 'yan makwannin da suka wuce, kasashen Afirka dake da karfin binciken cutar sun karu daga 2 zuwa sama da 10.

Kokarin da Sin ke yi na yaki da cutar, ya nuna yadda ya kamata babbar kasa dake sauke nauyin kanta ta yi. (Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China